13 Agusta 2020 - 13:31
Sojojin Sahayoniya Sun Kama Palasdinawa 10

Tashar talabijin din ‘Palastine Today” ta bayar da labarin cewa, ‘sojojin HKI sun kai farmaki a cikin sassa daban-daban na yankin yammacin kogin Jordan, inda su ka yi awon gaba da Palasdinawa 10.

ABNA24 : Kamen ya biyo bayan taho mu gama mai tsanani da aka yi a tsakanin sojojin’Yan Sahayoniya da kuma samarin Palasdinawa bayan hare-haren da ‘yan sahayoniyar su ka kai.

Shedun ganin ido sun ce, sojojin sahayoniyar sun yi amfani da albarusai masu rai akan samarin palasdinawan da ba su dauke da makamai.

Yankuna Palasdinawa dai sun saba da irin wannan farmakin da sojojin sahayoniya su ke kai wa daga lokaci zuwa lokaci, ba tare da wani dalili ba, tare da yin awon gaba da samarin palasdinawa.

Da akwai dubban palasdinawa a cikin gidajen kurkuku da su ka hada da kananan yara masu yawa.

342/